SALLAR ASUBAHI

“`SALLAR ASUBAHI sallah ce mai
muhimmanci. Allaah ya rantse da lokacinta a
cikin al-Qur’ani.
Allaah yace:-
( ﻭﺍﻟﻔﺠﺮ ﻭﻟﻴﺎﻝ ﻋﺸﺮ )
Saboda muhimmancin ta ne Allaah ya
kirata da sunan “QUR’AANUL FAJR”
Allaah yace:-
( ﺃﻗﻢ ﺍﻟﺼﻼﺓ ﻟﺪﻟﻮﻙ ﺍﻟﺸﻤﺲ ﺇﻟﻰ ﻏﺴﻖ ﺍﻟﻠﻴﻞ ﻭﻗﺮﺁﻥ
ﺍﻟﻔﺠﺮ ﺇﻥ ﻗﺮﺁﻥ ﺍﻟﻔﺠﺮ ﻛﺎﻥ ﻣﺸﻬﻮﺩﺍً )
Dan uwa zaka tauye wa kanka lada mai
yawa idan baka Tashi kaje ka sallace ta ba.
Zaka rasa darajoji masu dimbin yawa idan
ka gagara tashi don sallar ta.
Ka tuna fa itace Sallar da take wa
munafukai nauyi
Manxon Allaah (swallallaahu alaihi wa
sallam) yace Nafilar asubahi tafi duniya da
abinda yake cikin ta.
(( ﺭﻛﻌﺘﺎ ﺍﻟﻔﺠﺮ ﺧﻴﺮ ﻣﻦ ﺍﻟﺪﻧﻴﺎ ﻭﻣﺎ ﻓﻴﻬﺎ ( (
ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻛـــــــــــــ ـــــــــﺒﺮ
Idan har raka’atal Fajri tafi duniya da abinda
yake cikin ta, toh ya kake ganin ita kanta
Sallar Asubahin ??
KANA SON A DASA MAKA BISHIYA  A
ALJANNAH?
Manzon Allah (s.a.w) yace: “Duk wanda yace
‘Subhanallah, Walhamdulillah, Wala’ilaha
Illallah, Wallahu Akbar’, za’a dasa masa
bishiya a Aljannah da kowanne daya daga
cikin su”.
Silsilatul Ahaadiisus Sahiha 2880.
Me kake tsammani bayan ka idar da Sallah
ka zauna ka yi ta wadannan zikirorin?
Me kake zaton ma’anar za’a dasa maka
bishiya a Aljannah? Idan bishiyar taka ce
Aljannar da bishiyar ke ciki fa? Tabbas taka
ce.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s