Nigeria: Ƙaunar Buhari na neman hada faɗa

A Najeriya, yayin da aka ga kamun ludayin
gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari,
an fara samun saɓanin ra’ayi tsakanin
magoya bayansa sakamakon matakin da
wasu daga ciki ke ɗauka na sukar wasu
manufofin gwamnatinsa.
`Yan ga-ni-kashe-nin shugaban kasar dai na
cewa shugaba Buhari ba ya laifi, don haka
bai kamata a kushe masa ba, inda sukan
maida raddi da kakkausar kalamai idan ana
muhawara da su kai-tsaye ko ta shafukan
sada-zumunta na zamani, lamarin da ke
rage tagomashin shugaban kasar a zukatan
masu sassaucin ra`ayi.
Duk da cewa duka ƙaunar mutum guda ce
ta haɗa su, masu sassaucin ra`ayi na ganin
cewa ba daidai ba ne su yi shiru a duk inda
suka ga shugaban kasar ya yi kuskure,
saboda a ra`ayin irin waɗannan mutane,
mutum tara yake bai cika goma ba, don
haka kamar sauran jama’a, shugaban kasar
bai fi ƙarfin yin kuskure ba, kuma yi masa
gyara ko tsokaci wata siga ce ta ƙauna.
Sai dai ɓangaren shugaban kasar ya ce
demokradiyya ta gaji yabo da suka, don
haka babu dalilin fada da juna.
Masana dai na ganin cewa magoya bayan
shugaba Buhari na bukatar sake-lale a
muhawararsu, saboda masu sassaucin
ra`ayi na cewa azalzalar da `yan ga-ni-kashe-
ni ke musu ta sa ƙaunar da suke yi wa
shugaban kasar ta fara gushewa a hankali.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s