Ana Zargin Wasu Sun Wawure Biliyoyin Nerorin Gwamnatin Tarayya Na Sansanin ‘Yan Gudun Hijira.

Kwamitin da Majalisar Dattawa ta kafa na sa
ido akan kudaden da gwamnatin Najeriya
ke bayarwa domin sansanin ‘yan gudun
hijira ko IPDs ya ziyarci jihohin Borno da
Yobe domin gani da ido da kuma yadda aka
kashe kudade kimanin nera biliyan takwas
da gwamnatin Najeriya ta bayar.
Shugaban kwamitin Sanata Shehu Sani yace
gwamnatin tarayya ta bayar da fiye da nera
biliyan takwas domin taimakawa wadanda
suke sananin ‘yan gudun hijira a jihohin
arewa maso gabas da rikicin Boko Haram ya
daidaita.
To saidai a zagayawar da kwamitin yayi
Sanata Sani yace basu ga abun da aka yi na
a zo a gani ba a sansanin ‘yan gudun hijiran
da dimbin kudaden da gwamnatin tarayya
ta bayar da yanzu sun fi nera biliyan takwas.
Muryar Amurka na cikin wadanda suka
rufawa kwamitin baya lokacin da tawagar ta
ziyarci sansanonin ‘yan gudun hijira dake
cikin birnin Maiduguri.
Sanata Shehu Sani yayi karin haske akan
abun da suka gano.Yace gwamnatin tarayya
ta turo biliyoyin nerori amma babu yadda
za’a ga kudin a wuraren da suka kai ziyara.
Yace asibiti an ce wai sojoji ne suka kafa
suke kuma kula dashi. Makaranta Majalisar
Dinkin Duniya take yi. Kungiyoyi suke
taimakawa da abinci, inji Sanata Sani. Ya
tambaya yace ina kudin da gwamnatin
tarayya ta aiko suke tafiya.
Kudin ba ma na gine-gine ba ne, kudi ne na
a taimakawa ‘yan gudun hijira acewar Sani.
Shehu Sani yace wadansu mutane suna
anfani da ‘yan gudun hijiran suna tara ma
kansu dukiya a Abuja..Injishi wasu ma basu
taba zuwa yankin arewa maso gabas ba.
Shehu Sani yace mako mai zuwa zasu
gayyaci mutane da zara sun koma Abuja.
Yace duk wanda suka kama ya saci kudi
zasu sa a gurfanar dashi a gaban kotu.
Shi ma Sanata Malam Ali Wakili dake cikin
tawagar yace da mutum ya je sansanin zai
ga mutane suna cikin wani hali mai ban
tausayi musamman yadda mata da yara da
iyalansu suke, da yadda suke kokarin ciyar
da kansu ko saman ma kansu tufafi. Yara
basa zuwa makaranta mai kyau haka inda
suke kwanciya tamkar na dabbobi ne. Yace
wasu kungiyoyi ma sun mayar da ‘yan
gudun hijiran saniyar tatsa, sun zama abun
samun kudi.
‘Yan gudun hijiran sun tabbatar ba’a basu
abinci isasshe balantana ma samun kula mai
kyau.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s