Dan takarar APC ya lashe zaben gwamnan Ondo

Hukumar zaben Najeriya ta ayyana dan
takarar gwamnan jihar Ondo a karkashin
jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe
zaben jihar da aka yi ranar Asabar.
Rotimi Akeredolu ya samu kuri’a 244, 842,
yayin da mutumin da ke biye masa, dan
takara a karkashin jam’iyyar PDP, Eyitayo
Jegede ya lashe kuri’a 150,380.
Babban baturen zaben jihar Farfesa Ganiyu
Ambali, wanda ya bayar da sakamakon
zaben, ya kara da cewa mutum 1,647, 976
ne suka kada kuri’unsu.
Sai dai jam’iyyar PDP ta yi watsi da
sakamakon zaben, tana mai zargin hukumar
zabe da hada baki da jam’iyyar APC wajen
yin magudi.
Rotimi Akeredolu zai karbi mulki ne daga
hannun Olusegun Mimiko na jam’iyyar PDP,
wanda ya kwashe shekara takwas a kan
mulki.
Zaben na jihar Ondo ya ja hankalin ‘yan
Najeriya sakamakon kai ruwa ranan da aka
rika yi tsakanin jiga-jigan manyan jam’iyyun
biyu da ma masu son tsayawa jam’iyyun
takara gabaninsa.
Yanzu dai jiha daya ce kadai ta rage a
hannun jam’iyyar da ba APC ba a yankin
kudu maso yammacin Najeriya, wato jihar
Ekiti.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s