Wasu ‘yan fim sun yi tir da Nafisa kan Rahama Sadau.

Wasu daga cikin jaruman Kannywood sun yi
tir da kalaman da Nafisa Abdullahi ta rubuta a shafinta na Instagram cewa ba ta da wata alaka ta kawance ko ‘yan uwantaka da
Rahama Sadau.
Nafisa ta bayyana haka ne bayan wasu sun
yi ta kiraye-kiraye a gare ta da ta tsoma baki
domin a janye korar da aka yi wa Rahama
daga harkar fina-finan Hausa bayan an same
ta da laifin rungumar mawaki Classiq a wani
bidiyo da ya fitar.
Jarumar Kannywood, Ummi Ibrahim, wacce
aka fi sani da suna Zee Zee ta yi wa Nafisa
raddin cewa abin da ta yi bai kamata ba.A cewarta, “Ciwon ‘ya mace na ‘ya mace ne;
ko ba kwa shiri da ita bai kamata ki nunawa
duniya ba, don wannan rubutun da kika yi
wani zai yi zaton ba kya son (Rahama) ne”.
Zee Zee ta kara da cewa matsalar da ta shafi
Rahama ta shafi dukkan masu yin fina-finan
Kannywood domin kuwa idan abin zagi ta yi
dukkan su za a zaga ba ita kadai ba.Ita dai Nafisa Abdullahi ta yi ikirarin kowa ta
kansa yake yi tsakanin ‘yan kannywood,
tana mai cewa lokacin da wani ya wallafa
hotonta sanye da gajeren wando—batun da
ya janyo mata zage-zage—babu wata ‘yar
Kannywood da ta fito ta kare ta duk da yake
sun san cewa an yi ne domin a bata mata
suna.
A cewarta, “Ina mamakin yadda masu
amfani da shafin Instagram ke daukar mu
[‘yan fim] wallahi. Ya kamata ku sani cewa
da ni da Rahama sana’armu guda, amma
babu abokantaka ko ‘yan uwantaka
tsakanimu. Kai, babu wata dangantaka
tsakaninmu mata ‘yan fim. Don haka, duk
wanda yake tunanin muna jituwa yaudarar
kansa kawai yake yi.”
Ta kara da cewa ta yi amanna Rahama za ta
iya jure wa halin da ta fada a ciki, sannan ta
yi kira ga mutanen da ke son ta bi sahun
masu kiraye-kirayen a janye korar da aka yi
wa Rahama su daina bata lokacinsu.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s