Obasanjo Ya Soki Buhari Akan Yunkurin Ciwo Bashi daga Waje.

A wata lakcar tunawa da Chief Akintola
Williams tsohon shugaban kasa Olusegun
Obasanjo ya soki gwamnatin Muhammad
Buhari da kakkausan lafazi domin yunkurin
ciwo bashi daga waje na dalar Amurka
biliyan talatin
WASHINGTON DC —
Chief Obasanjo ya kuma soki gwamnatin
Buhari dangane da matsalolin da kasar ke
fama dasu a arewa maso gabashin kasar
wurin yaki da ta’adancin Boko Haram na
cewa sojojin Najeriya sun yi abubuwa na
asha kuma na kunya.
Amma kuma a wani hannun Obasanjo ya
jinjinawa gwamnatin akan yakin da ta keyi
da cin hanci da rashawa musamman a
bangaren alkalan shari’a. Ya kuma kira
gwamnatin Buhari da ta duba wasu sassan
musamman bangaren ‘yan majalisa.
Ya kira gwamnatin Buharin da ta daina
ratayawa gwamnatin baya duk matsalolin
da kasar ke fuskanta yau. Yace dama sabili
da matsalolin ne aka zabi gwamnatin domin
ta kawo canji.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s