Tsarin Electoral College Ya Sa Trump Ya Lashe Zaben Shugaban Kasar Amurka.

A zaben shugaban Amurka da aka gudanar
kawo yanzu kidgdiga na nuni da cewar
Hillary Clinton ta wuce shugaban kasa mai
jiran gado Donald Trump da ya ci zaben
zuwa fadar White House da kuri’u miliyan
biyu. Amma shi yayi nasara ne saboda ya
samu kuri’un Electoral College masu yawa
fiye da Hillary Clinton abun da ya sa ya
zama shugaban kasa na 45.Yayinda ake cigaba da kirga kuri’u a wasu
jihohi, bisa ga lissafin jiya Laraba Hillary
Clinton nada kuri’u 2,017,563 fiye da Trump
kuma zasu cigaba da karuwa saboda akwai
kuri’un da har yanzu ba’a kidayasu ba a
wasu jihohin da ta ci, musamman jihar
California, jihar da ta fi kowace jiha girma da
take yankin Pacific.
Ko menene ma ya faru, ko ta yaya kuri’unta
suka karu, kuri’un da Clinton ta samu ba
zasu canza sakamakon zaben da aka yi
ranar 8 ga wannan watan Nuwamba ba.
Zata zama ‘yar takara ta biyar a tarihin
Amurka, kuma ta biyu cikin shekaru 16 da
suka gabata da ta fi samun kuri’u amma
kuma ta kasa cin zaben saboda Electoral
College da aka kafa shekaru dari biyu yanzu.
Kundun tsarin mulkin kasar ya dorawa
Electoral College ikon zaban shugabannin
kasar.
Zaben shugaban kasa a Amurka ya rataya ne
akan kowace jiha da gundumar
Kwalumbiya, wato Washington babban
Birnin kasar. Duk wanda yaci kowace jiha
zai samu kuri’un Electoral College na wannan
jihar. Misali,idan jiha nada kuri’n Electoral
Cllege 10 kawai komi girmanta, dan takarar
da ya lashe zabe a jihar ya samu Electoral
College goma ke nan. Babu kari babu ragi.
Saboda haka kafin a ce mutum ya ci zaben
shugaban kasa to dole sai ya samu kuri’un
Electoral College 270 cikin jimillar 538. Jihar
da ta fi girma ita ce take da kuri’un Ellectoral
College ma fi yawa.
Trump ya ci jihohi da dama da ‘yar rata
yayinda Clinton, tsohuwar sakatariyar
harkokin wajen Amurka wadda ta kyautata
zaton zata zama shugabar kasa mace ta
farko ta lashe kuri’un manyan jihohin
California da New York. Nasara a wadannan
jihohin ta sa ta fi Donald Trump kuri’u amma
kuma zai karkare da kuri’un Electoral College
306 yayinda da ita kuma zata tashi da kuri’u
232 bayan da aka kammala kiyadayar duk
kuri’un.
Trump hamshakin attajiri wanda biloniya ne
yanzu yana fama da nada mukarrabansa da
zasu yi aiki dashi a sabuwar gwamnatinsa.
Ya taba yin tur da yin anfani da Electoral
College wajen zaban shugabannin kasar sai
dai kuma yace wata dabara ce dake da
mahimmanci domin ta ba kananan jihohi
damar yin tasiri a zaben shugaban kasa.
Ranar Talatan nan ya gayawa manema
labaran jaridar New York Times cewa shi ya
fi son yayi anfani da kuri’un jama’a kawai.
Yace shi bai taba son Electoral College ba
kafin yanzu saboda ta yin anfani da hanyar
ce ya zama Shugaban Kasa Mai Jiran Gado

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s