Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar da Jegede A Matsayin Dan Takarar Gwamnan Ondo Na PDP.

Kotun daukaka kara ta kawar da Jimoh
Ibrahim dan takarar gwamnan Ondo a
bangaren Modu Sherrif ta tabbatar da
Jegede na bangaren Ahmadu Makarfi.Hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke
ya ba Jegede damar tsayawa zaben
gwamnan Ondo wanda za’a gudanar ranar
Asabar 26 na wannan watan.
Shugaban kwamitin amintattun jam’iyyar
PDP Sanata Walid Jibrin yace zargin cewar
bangaren shari’ar kasar ya lalace to bai
lalace ba domin shari’a ta kawar masu da
Modu Sheriff. Yace sun gyara masu shi. Yace
mutanensu suna murna ba kadan ba.
Inji Jibrin alamomi sun nuna zasu ci zaben
domin mutane suna murna da hukumcin
kotun. Yace ko hukumar zabe ta kara lokaci
ko kada ta kara ba dan takararsu, Jegede zai
ci zabe.
Saidai Jibrin yayi tababan samun lokacin da
dan takaran nasu yake dashi na cika duk
takardun da ake bukata ya cika nan da ranar
Asabar da za’a yi zaben. Yace da so samu ne
to a kara masu lokaci.
Mutanen bangaren Modu Sheriff sun ce su
basu ga hukumcin ba saboda haka ba zasu
bayyana matakan da zasu dauka ba sai sun
karanta hukumcin.
Hukumar zabe tace duk hukumcin da kotun
ta yanke dashi zata yi aiki.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin
bayani.
Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar da Jegede
A Matsayin Dan Takarar Gwamnan Ondo Na
PDP

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s