Cikin Watanni Uku An Kashe ‘Yansandan Najeriya 128.

Alhaji Ibrahim Idris babban sifeton
rundunar ‘yansandan Najeriya yace cikin
watanni uku da suka gabata jami’ansa 128
aka kashe a sassan kasar daban daban
WASHINGTON DC —
Babban sifeton ya dora alhakin kashe
jami’an a kan masu tsatsauran ra’ayin
addini da ‘yan fashi da makami da wasu
‘yan tsagera.
Sanarwar da hedkwatar ‘yansandan dake
Abuja ta fitar tace wasu daga cikin aika
aikan an tafkasu ne a jihohin Zamfara da
Anambra da Rivers. Rundunar ‘yansandan
tace dole ne a daina hakan daga yanszu.
Kakakin rundunar matamakin kwamishanan
‘yansanda Don Aruna yace babban sifetonsu
bai ji dadin yadda ake kashe jami’ansa ba da
afkawa ofisoshinsu da motocinsu da ma
sauran gine-ginensu.
Yace duk inda aka samu tashin hankali
‘yansanda ne ke fara zuwa wurin. Yace wani
lokaci idan mutane nada damuwa
tsakaninsu da zara sun ga dansanda sai su
afka masa kamar shi ne umalubaisan
matsalarsu. Yace babban aikinsu shi ne
tabbatar da zaman lafiya da tsaro tare da
kare dukiyoyin jama’a.
A cewar Ambassador Yusuf Mamman kashe
dansanda babbar magana ce. Yace duk
wanda ya taba dansanda ya taba hukumar
Najeriya ne. Kamata yayi duk wanda ya
kashe dansanda koina ya shiga an je an
kamoshi.
Wani mai sharhi akan alamuran kullum Baba
Yola Muhammad Tango yace ‘yansandan
Najeriya na bukatar samun horo irin na
zamani. Yace rai rai ne kuma ‘yansanda suna
kashe mutane kullum amma babban sifeton
bai taba fitowa yayi magana ba a kai.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s