Shugaban Amurka Mai Jiran Gado Ya Fara Sauya Matsayinsa

Akwai alamar cewa sabon shugaban
Amurka dake jiran gado Donald Trump yana
ta kara janye jikinsa daga wasu daga cikin
alkawurran da ya dauka a lokacin yakin
neman zaben da yayi – ciki harda alwashin
da ya dauka na cewa zai jefa abokiyar
takarar tashi Hilary Clinton a kurkuku.
A lokkacin ganawar da yayi da manyan
editocin kafofin watsa labarai da dama ya
sha saka kafarwando daya da su, ciki har da
New York Times wacce ya sha la’anta, nan
ma Trump ya chanja matsayinsa, inda yace
yanzu yana mutuntua NY Times din, kuma
ma yana karanta ta.
A wajen wannan haduwar ce yake nunawa
kafofin watsa labaran cewa yanzu baya da
wata niyyar neman a gudanarda wani
bincike kan anfani da hanyar sadarwar
kanta da Hilary Clinton tayi anfani da ita
wajen aika sakkonin email a lokacinda take
rike da mukamin SHWA, balle kuma maganar
gidauniyar Clinton ta bada tallafi. Trump yace
Hilary ta ji jiki matuka, ita da iyalinta sun sha
bakar wahala a lokacin yakin neman zaben
da ya bayyana a matsayin “mai wahala
matuka.”
Tsohon M/garin New York, Rudy Giuliani,
daya daga cikin manyan mukarabban
Donald Trump wanda ma ha rake sa ran
cewa za’a bashi wani babban mukami a
sabuwar gwamnatin, yace kudurin Trump
din daidai yake da abinda aka saba gani a
siyasar Amurka:
Giuliani yace: “Abinda aka saba ne na al’adar
siyasar Amurka, cewa in kayi galaba a zabe,
sai ka manta wasu abubuwa, saboda haka
in abinda Trump ya yanke shawaran yi ke
nan, wannan daidai yake da abinda tarihin
siyasa ya gada ke nan a Amurka.”
Ita ma maganar chanji da dumamar yanayi,
wacce a lokacin kyampen, Trump yace kire-
kiren China ne, yanzu ya chanja matsayinsa a
kanta; a maimakon adawa, Trump yace ya
fasa janye Amurka daga cikin Yarjejeniyar
Kiyaye Yanayi ta Paris.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s