News

Nigeria ta kulla yarjejeniyar gina hanyar kankare da Dangote.

Gwamnatin Najeriya ta kulla yarjejenniya da
kamfanin Dangote domin gina hanyar
kankare mai nisan kilomita 42 daga garin
Obajana zuwa Kabba a jihar Kogi.
A yammacin ranar Talata ne bangarorin biyu
suka sanya hannu kan kwangilar a Abuja.
Babban sakatare a ma’aikatar ayyuka da
gidaje da wutar lantarki Injiniya Magaji
Abdullahi Gusau ne ya rattaba hannu a
madadin gwamnatin tarayyar.
Yayin da mai bai wa shugaban kamfanin na
Dangote shawara Injiniya Joseph Makoju ya
sa hannu a madadin kamfanin, yana mai
cewa “babban cigaba ne a tarihin Najeriya”.
Kamfanin na Dangote zai kashe kimanin
Naira biliyan 11 da rabi a aikin, amma an ba
shi aikin ne a madadin biyan kudin haraji na
sama da Naira biliyan biyar.
Kamfanin ya ce watanni 24 ne lokacin da
aka amince kare kwangilar, amma ya ce ya
kudiri aniyar kammala wa a cikin watanni
16.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out / Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out / Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out / Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out / Change )

Connecting to %s