Gwamnatin Nigeria Zata Iya Saukar da Farashin Dala ta Hanyar Anfani da Karfi?

Masana harkokin tattalin arziki na ci gaba
da fashin baki dangane da hauwahawar
farashin takardun kudi na Dala a Najeriya,
duk kuwa da kamen da Jami’an tsaro na
kasar ke yiwa ‘yan canji a kasuwannin
musayar kudade a birnanen Kano da
Abuja da kuma Lagos.
WASHINGTON, DC —
Kimananin ‘yan canjin kudi su 100 jami’an
tsaro na farin kaya suka cafke a kasuwar
musayar kudaden waje ta Wafa ta Kano bisa
tuhumar yin zagon kasa ga manufar
gwamnati ta dakile hauhawar farashin Dala.
Gabanin sumamen na Kano jami’an tsaron
sun kai makamancinsa a Lagos da Abuja.
Daya daga cikin masu hada hada a kasuwar
canjin ta Wafa, Adamu Isa Dan Juma, ya
nuna rashin jin dadinsa ga sumamen da
jami’an suka kai ba, kasancewar yanzu ana
mulkin dimokaradiyya amma akai irin
wannan sumamen kan mai uwa da wabi.
Shi kuma sakataren kungiyar masu canji ta
Najeriya shiyyar Arewa maso Yamma, Alhaji
Yusuf Dan Gama, na ganin karancin
takardun kudade na Dala shine babban abin
da ya haddasa wannan matsala. Amma a
zamansu da gwamnati tayi alkawarin samar
musu da ita, su kuma zasuyi kokarin hana
tashin farashin Dala.
Masanin tattalin arziki kuma shugaban
sashen nazarin harkokin banki da kudi a
kwalejin fasaha ta Kano, Mallam Lawan
Habib, na ganin amfani da kudi ba zai sa
gwamnati ta cimma burin na karya farashin
Dala ba, kasancewar ba gurin gwamnati
suke samun kudaden Dalar da suke bukata.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s