ALUMMAR KIRU/BEBEJI SUN KAI MAJALISAR WAKILAI KARA KOTU.

Kwanakin baya ne lokacin rikicin cogen da
aka ce ‘yan majalisa sun yiwa kasafin kudin
bana Abdulmummuni Jibrin ya fito ya zargi
majalisa da yin magudi lamarin da ya sa
suka dakatar dashi har na tsawon kwanaki
180
WASHINGTON DC —
A karshen makon da ya gabata ne wasu
mutane su 29 suka wakilci al’ummar
kananan hukumomin Kiru da Bebeji wajen
kai majalisar wakilan Najeriya kara kotu
akan dakatar da mai wakiltarsu Onarebul
Abdulmummuni Jibrin.
Barrister Muhammad Bashir Muntaka shi ne
lauyan al’ummar. Yace mutanen da suka zabi
Abdulmummuni Jibrin sun gaji da zama
basu da wakilci a majalisar. Mutanen suna
ganin dakatar da dan majalisar har na
tsawon kwanaki 180 an sabawa ka’ida.Inji
Barrister Muntaka babu wata doka da ta
baiwa majalisar ikon dakatar da wani dan
majalisar fiye da kwanaki 14. Babu wata
doka da ta amince da kwanaki fiye da haka.
Hakazalika Barrister Muntaka ya fayyace
abubuwan da al’ummar Kiru da Bebeji ke
bukata daga kotun. Suna son kotun tace
dakatarwar da aka yiwa Abulmummuni
Jibrin bata kan ka’ida. Kotu kuma ta biyashi
kadu da hakkin da aka tauye masa na
kwanakin da aka dakatar dashi.
Abdullahi Bulama lauya dake Kano ya yaba
da yunkurin mutanen. Yace abun da suka yi
zai karawa dimokradiya armashi kuma zai
ba na baya su san iyakar karfin majalisar.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari da karin
bayani.
Al’ummar Kiru da Bebeji dake Jihar Kano Sun
Kai Majalisar Wakilan Najeriya Kara Kotu – 2’
36

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s