ZA’A KAFA HUKUMAR RAGE RADADIN TALAUCI A NIGERIA

Majalisar Dattawan Najeriya zata hada
gwiwa da Majalisar Wakilai domin a kafa
hukumar da za ta rage radaddin talauci a
kasar.
WASHINGTON, DC —
Majalisar Dattawan Najeriya ta amincewa
bangaren zartarwa da ta bude wata
hukuma ta musamman wadda zata kula da
batun talauci da kasar ke fama da ita.
Shugaban kula da harkokin rage radadin
talauci a Majalisar Dattawa, Sanata Ali Mallam
Wakili, yace za a rage zafin talaucin ne ta
hanyar samarwa da mutane aikin yi. Amma
yace da farko sai mutane sun tsarkake
zukatansu kafin kawar da mutuwar zuci
wanda yayi katutu.
Ganin cewa gwamnatoci da suka shude
sunyi irin wannan yunkurin a baya, Mallam
Wakikli yace an za a kirkiri ma’aikatar ne
domin kyautata kudaden da suke fita, domin
sanin ina suka nufa kuma a hannun su waye
aka dankawa.
A cewar wata ‘yar Najeriya a Abuja, ba
talauci ke damun mutane a Najeriya ba,
rashin wadatar zuci ne idan har za a kafa
wannan hukuma a saka mutane na kwarai
to tabbas zata bayar da goyon bayanta.
Yayin da wakiliyar Muryar Amurka Medina
Dauda ke jin tabakin wasu ‘yan Najeriya, sun
bayyana jin dadinsu ga wannan kokari na
Majasa, domin suna ganin zai taimaka wajen
rage radadin talauci a kasar.
Domin karin bayani.
Za A Kafa Hukumar Rage Radadin Talauci A
Najeriya

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s