KUDIN DA MANCHESTER UNITED TAKE SAMU YA RAGU.

Kudin da Manchester United take samu ya
ragu sakamakon kasa samun cancantar
shiga gasar cin kofin Zakarun Turai ta Uefa,
ta bana da ta yi.
Kudin da kungiyar take samu a cikin
watanni uku na farkon shekara zuwa 30 ga
watan Satumba ya ragu da fam miliyan 3.4,
(kashi 2.8 cikin 100).
Haka kuma kudin da take samu a ranar da
take yin wasa ya ragu da kashi 32.3 cikin
100, inda kenan take samun fam miliyan
16.8. Ribar da take samu ta zama fam
miliyan 6.2.
Abin da ya fi haddasa raguwar kudin da
kungiyar ke samun shi ne, kasancewar
wasannin da take yi a gida sun ragu da
guda uku, idan aka kwatanta da wasannin
da ta yi a daidai wannan lokaci a 2015.
Bashin da ake bin ta kuma ya karu ne da
kashi 18 cikin dari zuwa fam miliyan 337.7,
sakamakon faduwar darajar kudin Ingila,
fam a kan dala tun lokacin da aka kada
kuri’ar ficewar Burtaniya daga kungiyar
Tarayyar Turai.
Babban darektan kungiyar ta Man United Ed
Woodward, ya ce, ” Yanayin kudin da muke
ciki a wannan lokaci ya nuna tasirin rashin
shigarmu gasar cin kofin Zakarun Turai ta
Uefa.”
Sai dai kuma kudaden da kungiyar take
samu na tallace-tallace ya karu da kashi 4.4
cikin dari zuwa fan miliyan 74.3, inda ake sa
ran kudin da take samu gaba daya a
shekara ya kai tsakanin fam miliyan 530 da
miliyan 540.
Kungiyar ta sayi ‘yan wasa hudu a lokacin
kasuwar sayen ‘yan wasa da ta wuce,
wadanda suka hada da dan wasan tsakiya
na Faransa, Paul Pogba, wanda ya kasance
mafi tsada a duniya kan fam miliyan 89 da
kuma dan Sweden Zlatan Ibrahimovic.
Man United din yanzu ita ce ta uku a tebur
din Premier, sannan ta kai wasan dab da na
kusa da karshe na cin kofin kalubale na Lig
(EFL Cup) na Ingila, amma kuma tana cikin
hadarin kasa kaiwa zagayen sili daya kwale
na gasar cin kofin Zakarun Turai na Europa,
yayin da ya rage wasanni biyu.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s