NIGERIA: ‘YAN SANDA SUNYI ARANGAMA DA ‘YAN SHI’A A KANO

Akalla mutane takwas aka kashe lokacin
da ‘yan sanda suka yi arangama da ‘yan
Shi’a a wajen birnin Kano na Nigeria, yayin
da aka kashe wani dan sanda daya.
Jami’an tsaro sun ce daya daga cikin ‘yan
sandan na nan rai a hannun Allah.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ambato
wani mutum yana cewa ya ga gawarwakin
mutum goma.
TALLA
Ads by Google
Ad covers the page
Stop seeing this ad
Wani dan jarida da ke tafiya da ‘yan Shi’ar ya
shaida wa BBC cewa ‘yan sanda sun harbi
mabiyansu da dama, kuma akwai fargabar
an kashe mutane da yawa.
Wani ganau ya shaida wa wakilinmu Yusuf
Ibrahim cewa ya ga motocin ‘yan sanda
dauke da mutane hudu da harin ya shafa,
amma ba tabbas ko sun mutu ko suna raye
ba.
Kungiyar ta ‘yan Uwa Musulmi, wacce ke
goyon bayan kasar Iran, na da tarihin yin
fito-na-fito da jami’an tsaron Nigeria.
Akalla magoya bayanta 349 aka kashe a
watan Disamban bara lokacin wata
arangama da suka yi da sojoji a garin Zaria.
‘Yan sanda sun tabbatar da rikicin na baya-
bayan nan, amma kakakinsu a jihar Kano
Magaji Majiya ya ce har yanzu suna tattar
bayanai.
Sai dai wani jami’i da bai yarda a bayyana
sunansa ba ya ce sun bude wuta ne saboda
‘yan Shi’ar sun kai musu hari.
Ya kuma kara da cewa ana ci gaba da bata-
kashin.
Yanzu haka an toshe babbar hanyar shiga
garin Kano daga kudu, da kuma fita zuwa
babban birnin kasar Abuja saboda rikicin.
Mabiya Shi’ar na yin tattakin da suka saba yi
ne a duk shekara zuwa garin Zaria, mai
nisan kilomita 165, inda nan ne cibiyar
kungiyar ta su.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s